Kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na duba yiwuwar korar ministan Abuja Nyesom Wike daga jam’iyyar, bisa bayanai da Daily Trust ta tattaro daga manyan majiyoyi a jam’iyyar.
Majiyoyin sun bayyana cewa da alama shugabannin jam’iyyar sun kai matakin gajiya da rikicin cikin gida da suke zargin Wike da haddasawa, kuma idan kokarin sulhu da kwamitin da Adolphus Wabara ke jagoranta ya ci tura, za a kori Wike daga jam’iyyar.
Wani jigo a jam’iyyar ya ce Wike ya nuna cewa sai ra’ayinsa kawai ake bi, kuma dukkan gwamnonin da ke kusa da shi sun kasa lallasar sa, kana ya ce babu yadda za a bari mutum ya ci-gaba da zama jagoran PDP alhali yana goyon bayan shugaban kasa daga jam’iyyar APC.
Wani babban jigo a Arewa ya kara da cewa yawancin mambobin NWC karkashin jagorancin Umar Damagum sun fara cimma matsaya kan korar Wike da magoya bayansa, domin dukkan yunkurin sasanci da aka yi tun bayan zaben 2023 sun gaza kawo sulhu.
