Hukumar kula da harkokin man fetur ta Nijeriya NMDPRA ta sanar da cewa an dakatar da aiwatar da harajin kashi 15 cikin 100 na kayan da ake shigo da su na man fetur da Gas.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis, daraktan sashen yaɗa labaran hukumar George Ene-Ita, ya bayyana cewa shirin aiwatar da wannan haraji ba ya cikin tsarin gwamnati a halin yanzu.
Wannan na zuwa ne bayan rahotannin da suka nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sanya harajin kashi 15 cikin 100 ga man fetur da dizal da ake shiga da su ƙasar.
