Tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya Bukola Saraki, ya shawarci jam’iyyar PDP ta dakatar da shirinta na gudanar da babban taronta na kasa da aka tsara gudanarwa daga ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamban 2025 a Ibadan, jihar Oyo, saboda rikice-rikicen siyasa da kuma hukuncin kotu.
Saraki ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a daren Laraba, bayan ganawarsa da mambobin kwamitin sulhu na jam’iyyar karkashin jagorancin Ambasada Hassan Adamu, yayin da suka kai masa ziyara a gidansa da ke Abuja.
Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya ce duk da ƙoƙarin da shugabannin jam’iyyar ke yi wajen warware sabani, taron Ibadan ya shiga cikin rikicin siyasa da hukuncin kotu wanda zai iya lalata sahihancin sakamakon da za a samu daga gare shi.
