Gwamnan jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin shirya babban taron jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta yanke hukuncin gudanar da babban taron jam’iyya a garin Ibadan.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Gwamna Fintiri ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai, bayan wani muhimmin taron jiga-jigan jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.
Taron ya samu halartar Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, Amb. Umar Damagum, Bukola Saraki, kakakin jam’iyyar, Debo Ologunagba, da sauran manyan jiga-jigai a cikinta.
Fintiri ya ce taron ya tattauna muhimman batutuwa da dama, yana mai jaddada cewa zasu tafi Ibadan domin babban taronsu, kuma wannan kudiri ba zai canza ba.
