Shugaban ƙungiyar ma’aikatan majalisun jihohi ta Nijeriya (PASAN) a jihar Bauchi Adamu Yusuf ne ya sanar da hakan ranar Juma’a, bisa bin umarnin shugabancin ƙungiyar na kasa.
Yusuf ya ce yajin aikin na da nufin tilasta wa gwamnatin tarayya ta aiwatar da dokar ‘yancin kuɗi ga majalisun jihohi, wadda ake ganin za ta karfafa tsarin dimokuraɗiyya.
Ya yabawa Gwamna Bala Mohammed bisa matakin da ya ɗauka wajen tabbatar da ‘yancin kuɗi ga majalisar jihar, yana mai kiran gwamnati ta gaggauta aiwatar da dokokin da suka shafi walwalar ma’aikatan majalisu da tsarin mulki.
