Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya karkashin Bola Ahmed Tinubu na aiki tukuru domin kawo karshen yawan faduwar layin wutar lanyarki da kuma tabbatar da tsayayyen hasken wutar a fadin kasar.
Adelabu ya bayyana haka ne a Uyo, jihar Akwa Ibom, yayin da yake ganawa da manema labarai inda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar wutar lantarki, Muhammadu Mamman.
Ministan ya ce tun zuwan Gwamnatin Tinubu an fara aiwatar da sabon tsari domin rage faduwar turakun wutar lantarki, tare da bullo da hanyoyin gudanar da harkokin wutar ta hanya cikin inganci.
