Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiNa jagoranci yin sulhu da 'yan bindiga akalla 600 - Sheikh Gumi

Na jagoranci yin sulhu da ‘yan bindiga akalla 600 – Sheikh Gumi

Sanannen Malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya mayar da martani ga masu kira da a kama shi kan tsokacinsa game da matsalar ‘yan bindiga da tsaro, inda ya kare rawar da yake takawa wajen shiga tsakanin tattaunawa da kungiyoyin ta’addanci domin neman samun zaman lafiya.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Gumi ya dade yana bayyana kansa a matsayin wanda ke shiga tsakani tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga, sai dai wasu na zarginsa da kare ‘yan ta’adda saboda ya fi jaddada maganar tattaunawa maimakon amfani da karfin soja.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, malamin ya bayyana masu kira da a kama shi a matsayin marasa kishin kasa da basu son gaskiya, inda ya ce aikinsa na shiga tsakanin tattaunawa da ‘yan bindiga ba wani laifi ba ne, domin kokari yake yi wajen kawo karshen tashin hankali.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata