DCL Hausa Radio
Kaitsaye

NITDA ta gargadi Yan Nijeriya kan wata manhaja da ke satar bayanan asusun ajiya

-

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta Nijeriya, ta yi gargadi game da wata sabuwar manhaja da ke kawo cikas ga na’ura ‘Grandoreiro’ wadda batagari suka kirkira domin tattare bayanan asusun ajiyar al’umma a fadin duniya. 

Google search engine

A wata sanarwa da tawagar kar ta kwana ta hukumar NITDA ta fitar, ta bayyana manhajar ‘Grandoreiro’ a matsayin wata babbar barazana ga na’urori, domin a cewar ta, za a iya amfani da manhajar wajen sarrafa wata na’urar ta daban tare da sace muhimman bayanai da suka hadar da bayanan banki ko bayanan sirri.

NITDA ta kuma bayyana cewa, akan iya samun sabuwar manhajar ne ta hanyar sakwannin kar ta kwana wato Email da kuma shafukan yanar gizo, wanda da zarar mutum ya sauke akan na’urarsa ko wayar salula, shikenan manhajar ta ketare ikon tsaro, komai ka iya faruwa.

NITDA ta yi gargadin cewa ita dai wannan manhajar ka iya haifar da asarar kudi da kuma satar bayanan sirri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Alƙali ya yi barazanar soke belin Abdulrasheed Maina da ake zargin kan zambar N738.6m

Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Abuja, ta yi barazanar soke belin tsohon shugaban kwamitin garambawul a harkar fansho na ƙasa, Abdulrasheed Maina,...

Majalisar dattawa ta musanta Ć™in amincewa da aika sakamakon zaÉ“e ta na’ura

Bangaren ’yan adawa a Majalisar Dattawan Nijeriya ya fayyace a ranar Alhamis cewa Majalisar ba ta ƙi amfani da tsarin tura sakamakon zaɓe ta na’ura...

Mafi Shahara