Wannan ziyara ta zo ne bayan labarin mummunar harin da ‘yan bindiga suka kai makarantar a ranar 17 ga Nuwamba.
A cewar jaridar Punch, Egbetokun zai gana da gwamnan jihar, Nasir Idris, sannan ya yi jawabi ga jami’an rundunar ‘yan sanda da ke jihar.
Ziyarar tasa ta taso ne bayan ya yi wa Shugaba Tinubu bayanin tsaro, inda aka tattauna karuwar hare-hare da sace mutane a jihohin Kebbi, Neja da Kwara.
Rahoton ya ce manyan hafsoshin tsaro sun halarci taron, ciki har da babban hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyode, da Air Vice Marshal Kelvin Aneke, da Rear Admiral Idi Abbas, da sauran shugabannin rundunonin tsaro.
