Jigo a jam’iyyar NNPP Buba Galadima, ya soki matakin wasu gwamnatocin Arewa na rufe makarantu saboda karuwar sace-sacen dalibai, yana bayyana matakin a matsayin abin kunya da rashin hangen nesa.
Buba Galadima ya furta haka ne a lokacin da yake hira a gidan talabijin na Arise a inda ya ce matsalar tsaro da ta kunno kai musamman a jihar Neja da sauran jihohi ba dalili ba ne da zai sa a tsaida karatu.
Ya jaddada cewa abin da ya kamata shi ne ƙarfafa tsaro a makarantun da ke fadin Arewa, tare da yin amfani da fasahohin zamani wajen gano barazana tun kafin ta faru.
A cewarsa yawancin hare-haren na faruwa ne saboda rashin amfani da bayanan sirri da ake samu da wuri.
