‘Yan bindiga sun kai hari tare da sace mutane a ƙauyen Biresawa da ke cikin ƙaramar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano.
Lamarin ya faru ne daren Litinin, tsakanin ƙarfe 11 na dare zuwa 12 na dare.
Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa akalla mutane takwas aka yi awon gaba da su maza biyu da mata shida, har ya zuwa wannan lokaci ba a samu labarin inda aka kai su ba.
Majiyar ta ce maharan sun shiga ƙauyen ne dauke da bindigogi, ta kuma bayyana cewa mazauna yankin sun shai da wa jami’an tsaro tun kafin faruwar harin bayan samun rahoton wasu baƙin duskoki da suka shiga yankin.
A wasu ƙauyuka kamar Sarmawa, Yan Chibi da Gano ma an tabbatar da sace mutane fiye da goma yayin da kusan ‘yan bindiga 50 kan babura suka yi dirar mikiya a garuruwan.
