Gwamnatin Ghana ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau, tana mai bayyana shi a matsayin karɓar mulki ta hanyar saba wa doka da kuma barazana ga dimokuraɗiyya a Yammacin Afirka.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ranar 26 ga Nuwamban 2025, hukumomin Ghana sun ce juyin mulkin ya lalata tsarin siyasa bayan kammala zaben shugaban ƙasa da na majalisar dokoki da aka yi ranar 23 ga Nuwamba.
Rahotanni sun ce wannan juyin mulki ya dakile sanar da sakamakon zaben da aka shirya fitarwa ranar 27 ga Nuwamba.
Ghana ta nuna tsananin damuwa da bacin rai, tana mai kiran abin a matsayin yunƙurin take muradun jama’ar Guinea-Bissau, inda ta nemi a gaggauta dawo da mulkin dimukradiyya, tare da kira ga duk bangarorin ƙasar su mutunta tsarin dimokuraɗiyyar.
