Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya jajanta wa ‘yan kasuwa da al’ummar jihar Kano kan mummunar asarar ‘yan kasuwa suka yi a kasuwar Singer a karshen mako.
A yammacin ranar Asabar ne, wuta ta tashi a kasuwar har zuwa safiyar Lahadi, inda ta yi barna mai yawa a sashen kasuwar kayan abinci.
Shugaban kasar, wanda tun da fari ya tuntubi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin samun rahoton halin da ake ciki, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin tashinta, wanda ke yawan jefa ‘yan kasuwa cikin halin kunci kamar yadda Bayo Onanuga mai magana da yawunsa ya sanar.
