Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiA daina tsangwama da cin zalin yara - Sakon shugaba Tinubu na...

A daina tsangwama da cin zalin yara – Sakon shugaba Tinubu na ranar yara a Nijeriya

Shugaba Bola Tinubu ya jaddada kudurin gwamnatinsa na kare hakki tare da inganta jin dadin yara a Najeriya, wadanda ya ayyana a matsayin goben kasar.

A wani jawabi da ya fitar na bikin ranar yara ta 2025, Tinubu ya bayyana bukatar daukar matakin gaggawa don magance cin zali, da cin zarafin da yin watsi da ake yi w miliyoyin yara a fadin kasar.

Rahotanni sun nuna cewa kimanin kashi 65 cikin 100 na yaran da suka isa zuwa makaranta a Najeriya suna fuskantar wani nau’i na cin zarafi.

Akan wannan Shugaba Tinubu ya bayyana wasu tsare-tsare na kare yara da gwamnatin ta fito da su, da suka hada da inganta yanayin koyo, da tabbatar da cewa babu wani dan Najeriya da aka bari a baya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata