Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaA shirye nake na yi aiki a kowane matsayi da Shugaba Tinubu...

A shirye nake na yi aiki a kowane matsayi da Shugaba Tinubu zai bani – Tanko Almakura

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Tanko Al-Makura, ya bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki a duk irin matsayin da Shugaba Bola Tinubu ya nada shi, muddin hakan zai kawo cigaba ga jam’iyya da kasa.

A wata hira da ya yi da Trust TV, Al-Makura ya ce, “Idan Shugaban kasa ya ce min, ‘Al-Makura ina so ka dinga share teburina duk Litinin,’ zan je, in share, in tafi cikin farin ciki da gamsuwa.”

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kiraye-kirayen daga ‘yan bangaren CPC da yankin Arewa ta Tsakiya da a nada Al-Makura a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, bayan murabus din Dr Abdullahi Umar Ganduje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata