Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAbin murna ne yadda al'ummar Katsina suka tarbi Kashim Shettima - Gwamna...

Abin murna ne yadda al’ummar Katsina suka tarbi Kashim Shettima – Gwamna Radda

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gode wa al’ummar jihar bisa irin tarbar da suka yi wa mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima, yayin ziyarar kwanaki biyu da ya kai jihar.

 

Radda ya ce wannan goyon baya da jama’a suka nuna ba sabon abu ba ne, domin tun farkon tafiyarsa a siyasa suna tare da shi, lamarin da ke kara masa kwarin guiwar gudanar da ingantaccen mulki.

 

Gwamnan ya kuma ce duk nasarorin da gwamnatinsa ke samu, baiwa ce daga Allah tare da goyon bayan tawagarsa da kuma amincewar jama’ar jihar.

 

Ya kara da cewa hakan shi ne ginshikin sauye-sauyen da ake gani a fadin jihar Katsina.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata