Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAbuja na komawa cikin birane mafi kayatarwa a duniya karkashin shugabancin Bola...

Abuja na komawa cikin birane mafi kayatarwa a duniya karkashin shugabancin Bola Tinubu da Nyesom Wike, in ji wani tsohon dan majalisa

Chibudom Nwuche, tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilan Nijeriya daga shekarar 1999 zuwa 2003, ya ce babban birnin tarayya na kan hanyarsa ta zama cikin biranen duniya mafi kayatarwa a karkashin shugabancin Shugaba Bola Tinubu da Minista Nyesom Wike.

Mista Nwuche ya bayyana haka ne a Abuja, lokacin da ya raka ministan babban birnin tarayya ziyarar duba ayyukan da ake gudanarwa a cikin birnin, a shirye-shiryen kaddamar da bikin cika shekaru biyu na shugaban kasa Bola Tinubu.

Wasu daga cikin ayyukan sun hada da titin Kasuwa da Fada da aka kammala a Gwagwalada, sai titi mai nisan kilomita 15 da ya tashi daga A2 zuwa Pai da kuma na Pai zuwa Gumani mai tsawon kilomita 15.4 a karamar hukumar Kwali.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata