Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaAdadin kujerun APC ya kai 72 a majalisar Dattawa, daga guda 50...

Adadin kujerun APC ya kai 72 a majalisar Dattawa, daga guda 50 da take da su a 2023

Majalisar dattawa a Najeriya ta karɓi Sanatoci hudu daga jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC, lamarin da ya ƙara karfafa rinjayen APC a zauren majalisar.

Sanatocin da suka sauya sheka su ne: Sanata Ekong Samson daga Akwa Ibom South, da Sanata Etim Bassey Akwa Ibom North East, sai Sanata Francis Fadahunsi Osun East, da Sanata Olubiyi Fadeyi Osun Central.

Gidan talabijin na Channel ya tattaro cewa, bayan sauya shekar, APC yanzu tana da kujeru 72 a Majalisar Dattawa ta 10, daga 50 da ta fara da su a watan Yunin shekarar 2023.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata