Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a karamar hukumar Nguru ta jihar Yobe ya ƙaru daga 25 zuwa 29, kamar yadda hukumomin jihar suka sanar.
Sakatare a hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe (YOSEMA), Dakta Mohammad Goje, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Damaturu a ranar Litinin.
Ya ce an ƙara gano gawawwaki huɗu daga cikin kogin, yayin da mutane tsakanin 8 zuwa 10 har yanzu ake neman su, ya ƙara da cewa fasinjoji 13 da suka jikkata a hatsarin an ba su magani kuma an sallame su daga asibiti.
