Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaADC ta bai wa su Atiku wa’adin zama cikakkun 'yan jam'iyya

ADC ta bai wa su Atiku wa’adin zama cikakkun ‘yan jam’iyya

Jam’iyyar ADC reshen jihar Adamawa ta bayar da wa’adin zama cikakkun ‘ya’yanta ga tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal tare da wasu manyan ‘yan siyasa.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban jam’iyyar a jihar Adamawa Shehu Yohanna na cewa ADC ta bude kofar rajista a cikinta, kuma ta haka ne kawai za ta tabbatar da su waye ‘ya’yanta.

A cewar jam’iyyar, ta bai wa ‘yan siyasar tsawon lokacin daga yanzu zuwa karshen shekarar 2025 da muke ciki.

Wannan ya zo a daidai lokacin da uwar jam’iyyar ta kasa ta bukaci su Atiku su yanki katin zama cikakkun mambobi, domin ci gaba da tunkarar zaben 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata