DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeSiyasaADC ta sake yin barazanar fita zanga-zanga har sai shugaban INEC Amupitan...

ADC ta sake yin barazanar fita zanga-zanga har sai shugaban INEC Amupitan ya sauka

Jam’iyyar adawa ta ADC ta bukaci Farfesa Joash Amupitan ya sauka daga shugabancin INEC, tare da yin barazanar sake shiga zanga-zanga idan hakan bai faru ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito jam’iyyar ta bayyana haka ne yayin da take martani kan sabbin zarge-zarge da ake yi masa.

ADC ta zargi Amupitan da nuna bangaranci ga jam’iyyar APC, bisa wasu tsofaffin sakonnin da ake zargin ya wallafa a shafin sada zumunta.

Kodayake mai magana da yawun shugaban INEC, Adedayo Oketola, ya gargadi jama’a kan masu kirkirar asusu na bogi da ke yada bayanan karya domin bata sunan maigidansa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata