Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaADC ta yi watsi da batun ƙarin albashin shugaban ƙasa, gwamnoni da...

ADC ta yi watsi da batun ƙarin albashin shugaban ƙasa, gwamnoni da sauran manyan jami’an gwamnati a Nijeriya

Jam’iyyar ADC ta bayyana adawa da shirin ƙarin albashi ga masu rike da mukaman siyasa da hukumar RMAFC ta gabatar.

Jam’iyyar ta ce wannan mataki abin tozarci ne ga talakawan Nijeriya da ke fama da tsadar rayuwa, hauhawar farashin kayayyaki, da rashin ingantaccen tsarin albashi.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce albashin da ake bai wa manyan jami’an gwamnati da alawus- alawus ya zarce misali idan aka kwatanta da abinda talakawa ke samu.

Jam’iyyar ta jaddada cewa maimakon ƙarin albashi ga shugabanni, ya fi dacewa a mayar da hankali kan ƙara mafi ƙarancin albashi, tabbatar da biyan ma’aikata akan lokaci don rage wahalar da al’umma ke cike.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata