Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiAFCON 2025: CAF ta sanya Najeriya a 'rukunin C' mai kasashen...

AFCON 2025: CAF ta sanya Najeriya a ‘rukunin C’ mai kasashen Tunisiya, Uganda da Tanzania

 

Shugaban Nijeriya sanye da rigar Super Eagles

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta samu kanta a rukunin C bayan raba jadawali na rukuni a gasar Kofin nahiyar Afrika,  AFCON ta 2025 da za a yi a kasar Morocco.

Daga cikin abokanan karawar ta Super Eagles a rukunin akwai kasar Tunisia sai Uganda da Tanzania.

Kasashen da ke rukunin A sun kunshi Morocco mai masaukin baki sai Mali da Zambia kana Tsibirin Comoros.

Daga rukunin B kasashen Masar wato Egypt da Afirka ta Kudu sai Angola da Zimbabwe ne za su kece raini.

Rukunin D akwai kasar Senegal da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango  sai Jamhuriyar Benin da Botswana.

Rukunin E na dauke da kasashen Algeria da Burkina Faso sai Equatorial Guinea da Sudan. Sai rukunin karshe na F mai kasashen Cote d’Ivoire kana Cameroun da Gabon tare da Mozambique.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata