Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAgushi zai kafa tarihin zama sinadarin girki na farko daga Nijeriya da...

Agushi zai kafa tarihin zama sinadarin girki na farko daga Nijeriya da zai je duniyar wata

Agushi, daya daga cikin sinadarin abinci a Nijeriya, na gab da kafa tarihi a matsayin abinci na farko daga Afirka ta Yamma da za a harba zuwa sararin samaniya, a wani bangare na binciken yadda abinci daga yankuna daban-daban na duniya zai iya jurewa tafiya da zama a sararin samaniya

Temidayo Oniosun, wanda ya kafa cibiyar Space in Africa, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi kai tsaye daga Cape Canaveral, jihar Florida, kusa da cibiyar sararin samaniya ta NASA.

Tun da farko an tsara a harba rokar da za ta tafi da shi ranar Alhamis, amma aka dage saboda yanayin guguwa. Sai dai an sake tsara harbar rokar zuwa ranar Jumu’a da misalin 4:45 na yamma agogon Nijeriya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata