Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAkpabio ya daukaka kara kan hukuncin kotu da ya maido da Sanata...

Akpabio ya daukaka kara kan hukuncin kotu da ya maido da Sanata Natasha majalisa

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya daukaka kara a Kotun Daukaka Kara da ke Abuja domin kalubalantar hukuncin da wata babbar kotu ta tarayya ta yanke na maido da Senata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ruwaito yadda kotun ta yanke hukunci a ranar 4 ga Yuli cewa dakatarwar wata shida da aka yi wa Natasha ta yi yawa, tare da tilasta biyan ta Naira miliyan biyar saboda wani rubutu da ta wallafa a shafin sada zumunta yayin da karar ke gudana.

A cikin korafinsa na hujjoji 11, Akpabio ya bukaci kotun daukaka karar ta soke hukuncin, yana mai cewa kotun farko ta sauka a layi, inda ta shiga hurumin shari’a kan harkokin cikin gida na Majalisar Dokoki kamar yadda kundin tsarin mulki na kasa (Sashe na 251) ya tanada.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata