Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAkwai bukatar kawo karshen karancin malaman makaranta cikin gaggawa - Remi Tinubu

Akwai bukatar kawo karshen karancin malaman makaranta cikin gaggawa – Remi Tinubu

Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta ce akwai bukatar a kawo karshen karancin malaman makaranta da ake fama da shi a fadin kasar cikin gaggawa.

Remi Tinubu ta bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai albarkacin ranar malamai ta duniya.

Jaridar Punch ta ruwaito Remi na bayyana malaman makaranta a matsayin jaruman da ke dora yara a kan turbar makoma ingantacciya.

Majalisar dinkin duniya ta ware duk ranar 5 ga watan Oktoba a matsayin ranar malamai, domin tunawa da irin gagarumar gudummawar da suke bayarwa wajen ci-gaban al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata