Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaAkwai wadanda suka cancanci tsaya mana takarar shugabancin Nijeriya a 2027 bayan...

Akwai wadanda suka cancanci tsaya mana takarar shugabancin Nijeriya a 2027 bayan Goodluck – PDP

Jam’iyyar PDP ta ce akwai wadanda suka cancanci tsaya mata takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2027, baya ga tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.

Sakataren jam’iyyar na kasa Debo Ologunaba ne ya bayyana haka, yana mai cewa PDP tana da gwamnoni da kuma wasu manyan ‘yan siyasa da suke da gogewar da za su iya tsaya mata takarar shugabancin ƙasar a zaben 2027 da ke tafe kasa da shekaru biyu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Haka kuma, ya ce babu wanda zai hana su gudanar da babban taron jam’iyya a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, wanda aka shirya gabatarwa a jihar Oyo.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata