Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAna hasashen ruwan sama mai karfiba jihohi 14

Ana hasashen ruwan sama mai karfiba jihohi 14

Ma’aikatar muhalli ta Najeriya ta fitar da gargadin yiwuwar samun ruwan sama mai karfin gaske a jihohi 14, wanda ka iya jawo fuskantar ambaliyar ruwa a wasu sassa.

Cikin wata sanarwa, daraktan da ke kula da sashen zaizayar kasa da kuma ambaliyar ruwa na ma’aikatar Usman Abdullahi Bokani, ya ce an yi hasashen samun ruwan ne daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Satumban 2025.

Kazalika ya bukaci masu ruwa da tsaki a dukkanin matakai su kasance cikin shirin ko ta kwana.

Jihohin da sanarwar ta bayyana sun hada da Ebonyi, Cross-River, Kano, Zamfara, Taraba, Abia da kuma Yobe.

Sauran sun hadar da jihohin Plateau, Borno, Imo, Niger, Sokoto, Kaduna da Akwa Ibom.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata