Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAkwai yiyuwar samun tsaikon tashin jiragen sama saboda yajin aikin da ma'aikatan...

Akwai yiyuwar samun tsaikon tashin jiragen sama saboda yajin aikin da ma’aikatan hukumar hasashen yanayi suka shiga a Nijeriya

Fasinjojin da ke filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas da filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, sun nuna damuwa kan matakin da ma’aikatan hukumar hasashen yanayi ta Najeriya na fara yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar daga daren ranar Talata.

Yayin da wasu fasinjojin ke cikin rudani game da lokacin da za a fara yajin aikin, da dama sun fara kokawa game da yiyuwar dakatar da tashin wasu jiragen saman, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito

Ma’aikatan sun shirya zanga-zangar ne, saboda zargin hukumar ta NiMet da gaza aiwatar da mafi karancin albashi, rashin biyan alawus din ma’aikata, da yin watsi da bukatar shigar da ma’aikatan da aka cire a tsarin albashi a baya, da dai sauransu.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata