Al’amura sun fara komawa daidai a Guinea Bissau bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sojoji sun nada Janar Horta N’Tam, a matsayin shugaban na rikon kwarya na tsawon shekara guda bayan kifar da gwamnati a ranar Laraba.
Rahoton ya ce juyin mulkin ya faru ne kwana guda kafin a bayyana sakamakon zaben 23 ga Nuwamba.
A safiyar Juma’a, motocin haya a manyan tituna sun dawo zirga-zirga, shaguna da kasuwanni sun fara budewa, duk da cewa har yanzu an tsaurara tsaro a wasu muhimman wurare.
