Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiAlbashi mafi kankanta na N70,000 ba zai wadaci ma'aikaci a Nijeriya ba...

Albashi mafi kankanta na N70,000 ba zai wadaci ma’aikaci a Nijeriya ba – NLC

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) tare da ma’aikatan gwamnatin tarayya sun bukaci a gaggauta duba sabuwar dokar albashin ƙasa, suna mai jaddada cewa albashin Naira 70,000 da ake biya yanzu ba zai iya ɗaukar nauyi ba.

Sun yi wannan kira ne, bayan wasu jihohi da dama a fadin ƙasar suka ɗauki matakin ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikatan su sama da N70,000, domin daidaita da halin tattalin arzikin da ake ciki.

Kungiyoyin kwadago da ma’aikatan da suka zanta da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a tattaunawa dabam-dabam, sun ce hauhawar farashi, tsadar abinci, sufuri, gidaje, da sauran aiyukan yau da kullum ya sa N70,000 ba zai iya ɗaukar rayuwa ba.

Shugaba Bola Tinubu dai ya sanya hannu kan sabuwar dokar mafi ƙarancin albashi a watan Yuli 2024, inda ya daga mafi ƙarancin albashin ƙasa daga N30,000 zuwa N70,000.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata