Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAl'ummar Shanono a jihar Kano sun koka kan hare-haren 'yan bindiga

Al’ummar Shanono a jihar Kano sun koka kan hare-haren ‘yan bindiga

Al’ummar Farin-Ruwa da ke ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano sun roƙi gwamnatin Nijeriya ta kawo musu dauki cikin gaggawa saboda hare-haren ‘yan bindiga da ake zargin suna shigowa daga jihar Katsina.

Jagoran al’ummar, Alhaji Yahaya Bagobiri, wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro na yankin, ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a Kano da yammacin Alhamis, inda ya ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane da dama da asarar dukiya da shanu a kauyukan Farin-Ruwa, Kuraku, Gorantuse, Saure da Shadu.

Bagobiri ya ce a harin baya-bayan nan an hallaka mutane da dama, an kuma sace akalla shanu 1,600 tare da lalata kayan jama’a, dalilin da ya sa mazauna yankin da dama suka fara barin yankin zuwa Kano da wasu wurare don neman tsira, yayin da ‘yan bindigar ke kai hari a kowane lokaci ba tare da tsoro ba.

Haka kuma ya ƙara da cewa wani daga cikin mutanen yankin da aka sace ya biya kudin fansa na naira miliyan 15 kafin a sake shi, inda ya koka da ƙarancin jami’an tsaro a yankin.

Ya roƙi gwamnatin Kano da ta haɗa kai da hukumomin tsaro da wakilan mazabar Bagwai/Shanono domin magance matsalar kafin ta ƙara muni.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata