Tuesday, April 7, 2026
HomeKetareAmbaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 30 a gabascin Indiya

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 30 a gabascin Indiya

Mamakon ruwan sama na tsawon kwanaki biyu ya haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa tare da yin sanadin mutuwar mutane akalla 30 a arewa maso gabashin Indiya.

Hukumomin agaji na kasar a wannan Lahadi, sun ce mutane takwas ne suka mutu a yankin Assam, wasu tara a Arunachal Pradesh, mafi yawa daga cikinsu zabtarewar kasa ce ta rutsa da su.

Mahukunta sun fitar da gargadi ga wasu gundumomin da dama a gabascin Indiya, saboda mamakon ruwan sama a cikin kwanaki da suka gabata.

Ruwan saman ya sa kogin Brahmaputra ya cika ya tumbatsa, wanda ya taso daga yankin Himalayas har zuwa kasar Bangladesh.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata