Wednesday, April 8, 2026
HomeKetareAmurka da Iran sun amince da tsagaita wuta

Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta

Kasashen Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta na makonni biyu, tare da shirin sake buɗe mashigin ruwan Strait of Hormuz mai muhimmanci ga harkar mai da iskar gas a duniya.

Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Tasnim sun tabbatar da cewa Iran ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutar da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce za a ba da damar wucewar jiragen ruwa cikin aminci a mashigin Hormuz na tsawon makonni biyu, bisa haɗin gwiwa da rundunar sojin ƙasar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya buɗe mashigin a matsayin sharadi na tsagaita wutar, inda ya yi barazanar kai hari kan bangaren makamashi da muhimman gine-ginen Iran idan ba ta bi yarjejeniyar ba.

Mashigin Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga jigilar mai a duniya, ya kasance kusan a rufe tun bayan harin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Wani babban jami’in Amurka ya ce Isra’ila ma za ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da Donald Trump ya kira “yarjejeniya mai bangarori biyu.”

A gefe guda, Jaridar The Nation ta ruwaito Pakistan, wadda ta taka rawa wajen sasanta rikicin, ta sanar da cewa tsagaita wutar ya fara aiki nan take tsakanin bangarorin biyu.

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya bayyana maraba da matakin, yana mai cewa an cimma yarjejeniya ta tsagaita wuta gaba ɗaya, har da wasu wurare kamar Lebanon.

Ya kuma gayyaci bangarorin biyu zuwa Islamabad domin ci gaba da tattaunawa da nufin kawo ƙarshen rikicin baki ɗaya.

Tun da farko, Donald Trump ya ce Shehbaz Sharif ya roƙe shi da ya dakatar da harin da ya yi niyyar kai wa Iran.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata