Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAmurka ta fara bibiyar 'yan Nijeriya da ke neman bizar karatu a...

Amurka ta fara bibiyar ‘yan Nijeriya da ke neman bizar karatu a kasar

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya sanarwar da wasu ‘yan Nijeriya masu neman izinin shiga kasar cewa dole ne su buɗe shafinsu na kafofin sada zumunta ga jama’a domin ba su damar binciken abubuwan da suke yi.

F, M, da J wasu nau’ikan biza da gwamnatin Amurka ke bayarwa ga daidaikun mutane da ke zuwa ƙasar don neman ilimi ko karantawa.

Ta bayyana cewa masu neman a cikin waɗannan nau’ikan dole ne a yanzu saita bayanan shafukansu na sada zumunta ga jama’a, a matsayin wani ɓangare na karbar buƙatar neman izinin shiga kasar.

Wannan na kunshe a cikin wani bayani a shafin ofishin Jakadancin Amurka na Najeriya, a cewar jaridar Punch.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata