Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce an soke sama da visa 100,000 tun bayan dawowar Donald Trump kan mulki, ciki har da kusan visa 8,000 na ɗalibai da visa 2,500 na ƙwararrun ma’aikata.
Gwamnatin ta ce matakan suna cikin sabon tsarin ƙarfafa tsaro da aiwatar da dokokin shige da fice.
Rahoton da DW Afrika ta ruwaito ya ce an fi soke visar ne saboda kuskurensu na tsawaita zama a kasar fiye da izini, tuƙi a yayin maye, kai wa jama’a hari, da kuma sata.
Hukumomin sun ce gwamnatin ta jagoranci korar mutane fiye da miliyan 2.5, abin da suke kallo a matsayin bajinta a tarihin kasar ta Amurka.
Sai dai rahotanni sun ce akwai wasu daga cikin waɗanda aka kora da suna da visa mai inganci, lamarin da ya tayar da ce-ce-ku-ce kan hakkokin ɗan adam da tauye tsarin doka wajen kamewa da korar baki.
