Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAn dakatar da jirgin Rano Air kan zargin matsalar inji - NCAA

An dakatar da jirgin Rano Air kan zargin matsalar inji – NCAA

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da wani jirgin Rano Air mai lamba 5N-BZY bayan fuskantar hatsarin gobara da matsalar injin a sama.

Gidan talabijin na Channels ya ruwato cewa jirgin, wanda ke kan hanya daga Kano zuwa Sokoto a ranar Lahadi, 29 ga Yuni, 2025, ya dawo filin jirgi bayan matuka sun gano hayaki a dakin tuki, lamarin da ya tayar da hankalin fasinjoji.

Kakakin hukumar ta NCAA, Michael Achimugu, ya bayyana cewa matukan jirgin sun sun yi gaggawar ankarar da masu kula da zirga-zirgar sararin samaniya, inda kuma aka ɗauki matakan kar ta kwana domin saukar da jirgin cikin aminci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata