Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiAn damke 'yan Nijeriya 5 a kasar Libya bisa zargin satar kayan...

An damke ‘yan Nijeriya 5 a kasar Libya bisa zargin satar kayan lantarki

Hukumomi a birnin Sabha na kasar Libya sun kama wasu ‘yan Najeriya biyar da ake zargi da satar kayan lantarki a wata gona.

Kungiyar Migrant Rescue Watch ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a shafukan sada zumunta a ranar Litinin, 26 ga Mayu, 2025.

A cewar rahoton, jami’an hukumar ‘yan sanda ta Al-Qahira ne suka cafke wadanda ake zargin a ranar Lahadi, 25 ga watan Mayu, kuma tuni an miƙa su ga sashen shari’a domin daukar mataki na gaba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata