Rundunar sojin ruwa ta Nijeriya ta tabbatar da cafke jami’anta da suka shiga yi fada da wasu jami’an tsaro a Jihar Bayelsa yayin ziyarar Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a bainar jama’a, inda wani bidiyo mai tsawon daƙiƙa 53 ya nuna yadda jami’an ke cacar baki cikin fushi kar da bai wa hamatta iska.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa rundunar ta ce an kama waɗanda abin ya shafa domin bincike da ɗaukar matakin ladabtarwa kan su.
