Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAn kama wani mai gari bisa zargin taimakawa masu garkuwa da mutane...

An kama wani mai gari bisa zargin taimakawa masu garkuwa da mutane a jihar Neja

An kama mai garin Guiwa, Garba Mohammed, tare da wasu mutane 13 bisa zargin tallafawa da kuma ba da kariya ga ‘yan bindiga da suka addabi yankin Mashegu na jihar Neja.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’a a wani sumame da jami’an ‘yan sanda da ‘yan bangar yankin suka kai, inda suka nufi sansanonin ‘yan bindiga da maboyarsu a kauyukan Guiwa da Telle.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa ana zargin Mohammed da bayar da a mafaka da kayan aiki ga masu laifin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata