DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeLabaraiAn kama 'yan Najeriya 106 a shekarar 2024 kan zargin safarar kwaya...

An kama ‘yan Najeriya 106 a shekarar 2024 kan zargin safarar kwaya a India

Rahotanni daga cibiyar da ke kula da harkar ƙwayoyi a India, sun tabbatar da cewa ‘yan Najeriya 106 na daga cikin ‘yan kasashen waje 660 da aka kama a shekarar da ta gabata, kan zargin su da safarar miyagun ƙwayoyi a kasar.

Yayin wani taron masu ruwa da tsaki da daga sassa daban daban na kasar, ministan cikin gida na India Amit Shah, ya ce’ yan kasar Nepal 203 aka kama, wadanda suka fi kowa yawa, sai kuma ‘yan Myanmar 25, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

Rahoton ya kuma ce akwai ‘yan kasashen Bangladesh 18, Ivory Coast 14, Ghana 13 sai kuma ‘yan Iceland 10 da aka kamar kan zarge-zargen tu’ammali da miyagun ƙwayoyin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata