Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAn mayar da namun dajin da aka samu gidan tsohon Akanta Janar...

An mayar da namun dajin da aka samu gidan tsohon Akanta Janar na Nijeriya zuwa gidan adana namun daji na Kano

Manajan Daraktan Gidan kula da namun na Kano, Sadik Kura Muhammad, ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewa an kamo kumurcin macijin da ya tsere daga gidan tsohon Akantan Janar na Nijeriya, Ahmed Idris, tare da sauran namun daji, inda aka mayar da su gidan zoo na Kano.

Shugaban Zoo ɗin, ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan rediyo, inda ya ce duk da cewa tsohon Akanta Janar ɗin na da lasisi, ganin yadda mazauna unguwanni irin su Daneji, Mandawari da Kabara suka shiga fargaba, ya yanke shawarar mika dabbobin ga gwamnati da kansa.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa an fara bincike, kuma an gayyaci Ahmed Idris domin yi masa tambayoyi kan lamarin.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa sun firgici a sakamakon tsoron macijin da ya tsere.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata