Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya rattaba hannu kan wata doka da za ta sa duk masu ababen hawa a kasar su sayi lasisin sanya rediyo kafin su yi inshorar motocinsu.
Dokar sabon harajin mai cike da cece-kuce, ta ce masu ababen hawa za su biya dala $92 duk shekara don sauraron rediyo a cikin motocinsu.
Masu sukar lamirin sun bayyana cewa harajin ya yi yawa, sai dai wani babban jami’in gwamnati, Nick Mangwana, ya ce sanya harajin ya zama dole.
