Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiAn sace dalibai 330 an rufe makarantun boko 52 a jihar Katsina,...

An sace dalibai 330 an rufe makarantun boko 52 a jihar Katsina, in ji rahoton Oxford Policy

Wani bincike da Oxford Policy Management ta gudanar ya nuna cewa tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025, akalla dalibai 330 aka sace a kananan hukumomi uku na jihar Katsina – Batsari, Faskari da Kankara.

Hadiza Tijani, wata masaniya daga Oxford Policy Management, ce ta bayyana haka a taron gabatar da sakamakon binciken da aka gudanar tare da goyon bayan UNICEF da ma’aikatar Ilimi ta Katsina.

Rahoton ya nuna cewa dalibai biyu aka kashe a wannan lokaci, haka kuma ma’aikatan makarantu 15 aka sace, biyar kuma aka kashe. A Kankara kadai, sama da dalibai 300 aka yi garkuwa da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata