Kwana guda bayan ceto ɗalibai mata 24 daga hannun ’yan bindiga, an sake samun rahoton sace mutane da dama a ƙauyen Kurmaci da ke Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu a Jihar Kebbi.
’Yan bindigar, kimanin su fiye da 30, sun kai farmaki a daren Laraba lokacin da mazauna yankin ke barci.
A yayin harin, an sace mutanen da ba a tantance adadinsu ba, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Wani mazaunin yankin Aliyu Dangaladima ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, wannan hari shi ne na uku da ƙauyen ya fuskanta cikin wata guda.
