Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaAn saka ranar da Sanata Natasha Akpoti za ta bayyana gaban kotu...

An saka ranar da Sanata Natasha Akpoti za ta bayyana gaban kotu bisa karar da gwamnatin Nijeriya ke yi mata

Dakatacciyar Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti-Uduaghan, za ta bayyana a kotu ranar Talata, kamar yadda aka bukata.

Jagoran lauyoyinta West Idahosa SAN, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Sai dai Idahosa ya bayyana rashin tabbas ko Gwamnatin Tarayya na da niyyar gurfanar da ita a ranar Talatar.

Ya ce duk da me Gwamnatin Tarayya ke shiryawa, Akpoti-Uduaghan, a matsayinta na mace mai bin doka, za ta yi biyayya ga umarnin kotu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata