Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaAn sake samun baraka a jam'iyyar ADC ta Nijeriya

An sake samun baraka a jam’iyyar ADC ta Nijeriya

Wani sabon tsagi ya ɓulla a cikin jam’iyyar ADC, inda ya yi watsi da sahihancin bangaren da David Mark ke jagoranta, tare da nesanta kansa da bangaren Nafiu Bala.

A cewar rahoton tashar AIT, sabon bangaren wanda Don Norman Obinna ke jagoranta, ya ce shi ne halastaccen Kwamitin Zartarwa na ƙasa na jam’iyyar.

Bangaren ya bayyana cewa ya shiga gaba domin tafiyar da harkokin jam’iyyar kafin babban taronta na ƙasa mai zuwa.

Jaridar Punch ta ambato wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda bangaren ya zargi cewa wa’adin mulkin tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, ya ƙare tun watan Agustan 2022, sannan daga baya ya fuskanci shari’o’i sakamakon ƙin sauka daga mukaminsa.

Haka kuma, bangaren ya bayyana cewa Nafiu Bala bai taɓa riƙe muƙamin mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa ba, tare da jaddada cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Dumebi Kachikwu, har yanzu yana cikin jam’iyyar.

Bangaren ya kuma sanar da nada shugabannin riƙo domin kula da harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da babban taron ƙasa da ke tafe nan gaba kadan a jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata