Friday, April 10, 2026
HomeLabaraiAn sako wasu mata 'yan Nijeriya bayan shafe watanni 10 tsare a...

An sako wasu mata ‘yan Nijeriya bayan shafe watanni 10 tsare a Saudiyya bisa zargin safarar kwayoyi

Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta sanar da sakin wasu mata uku ‘yan Nijeriya da aka gurfanar a kasar Saudiyya bisa zargin safarar miyagun kwayoyi, bayan sun shafe watanni 10 a tsare gidan kaso.
Sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar Kimiebi Ebienfa ya fitar, ta tabbatar da sako matan bayan an bi hanyoyin diflomasiyya.
A watan Maris na 2024 ne aka damke Hadiza Abba, da Fatima Umate Malah, da kuma Fatima Kannai Gamboil a filin jirgin saman kasa da kasa na Yarima Mohammad bin Abdulaziz da ke birnin Madinah.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata