An ce yunƙurin janye ƙudurin ya janyo cece kuce a yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa hayaniyar ta fara ne lokacin da shugaban kwamitin harkokin majalisa, Francis Waive, ya gabatar da buƙatar a janye amincewar da aka yi wa kudurin.
Ya ce an yi hakan ne domin a sake duba dokar don dacewa da sabbin gyare gyaren tsarin gudanar da zaɓe.
Francis Waive ya roƙi ‘yan majalisa sun janye wancan amincewa domin a mayar da kudurin gaban kwamitin don sake yin nazari akai.
