Sunday, April 5, 2026
HomeKetareAn tafi da 'yan jaridar Nijar zuwa Yamai bayan kama su da...

An tafi da ‘yan jaridar Nijar zuwa Yamai bayan kama su da sojin mulkin kasar suka yi

Hukumomin mulkin sojan Nijar sun tusa kewar ‘yan jaridar uku na Radio Sahara da suka kama a Agadez zuwa babban birnin Yamai.

Jami’an tsaron Gendarmerie na jihar Agadez sun yi wa ‘yan jaridar uku na Radio Sahara rakiya zuwa babban birnin Yamai bayan sun kwashe kwanaki hudu a tsare a hannun gendarmerie.

‘Yan jaridar dai uku da suka hada Hamid Mahmoud, Masaouda Jaharou da kuma Mahaman Sani an kama su ne da farko a daren 7 wayewar 8 ga watan Mayun nan biyo bayan yada wani labari da ke nuna cewa Nijar ta katse dangantakar tsaro da kasar Rasha.

An dai kuma saki ‘yan jaridar a ranar 9 ga watan Mayun bayan an gurfanar da su a gaban kotun jihar Agadez sai dai a daren wannan rana ta 9 wayewar 10 ga watan Mayun kuma jami’an tsaron Gendarmerie sun sake kama su da misalin karfe 3 na dare inda suka shafe kwanaki 4 kafin a yau a tusa kewar su zuwa babban birnin Yamai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata